Ministan kula da raya kasa da tattalin arzikin Jamus Gerd Müller ya bukatar girka tsarin nan na Plan Marshall kamar yadda aka yi wa kasashen Turai wajen tallafar tattalin arzikin su, bayan yakin duniya na biyu, hakan zai taimaka wajen yaki da kwararrar yan ci rani zuwa nahiyar Turai daga Afrika. A Najeriya kuwa an dauki sabon Salon hukunta wadanda ake zargi da almundahana.