Bayan labaran duniya, za a ji karin bayani kan taron sasanta manoma da makiyaya tsakanin Najeriya da Nijar a jihar Diffa na Nijar. Wani atisayen hadin gwiwa tsakanin rundunar soji da ta 'yan sanda a Ghana ya sake karbo ikon yankin Volta sa'o'i kalilan bayan masu rajin kafa kasar Togoland sun karbe ikon yankin.