A cikin shirin bayann kun sha labaran duniya, za ku ji cewar ilimin yara mata na ci gaba da tafiyar hawainiya a wasu kasashe na Afirka ciki har da Nijar da tarayyar Najeriya. Sai dai sarkin gudunmawar tasawa ya tashi tsaye don cire wa 'yan mata da ke da burin karatu kitse a wuta, lamarin da wadanda aka yi don su suka yaba.