A cikin shirin za a ji cewa hukumar lafiya ta Najeriya ta ce mutane sama da 450 ne suka kamu da cutar zazzabin bera wato Lassa Fever cikin makonni biyar na farkon wannan shekarar. A Nijar kuwa matakin rage radadin tsadar rayuwa ga talakawa gwamnatin kasar ta kaddamar da tsarin sayar da cimaka a farashi mai rahusa ga jama'a.