Bayan labarun duniya jigon rahotannin ya kasance kan makomar ilimi a Nijar. A birnin Legas na Najeriya ana zaman dar-dar bayan kashe wasu jami'an tsaro da wasu 'yan bindiga suka yi. A Kwango harkoki sun tsaya cak sakamakon wata zanga-zangar adawa da Shugaba Kabila.