Cikin shirin za a ji cewar dakarun kasar Mali sun kashe mutuna 14 da ake tsare da su bisa zargin ta'addanci, yayin da suka yi yunkurin tserewa daga hannun mahukunta a yankin tsakiyar kasar. Wannan matakin dai ya janyo suka daga kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya. Akwai ma shirin Ra'ayin Malamai da ya tattauna batun take hakkin jama'a a Jamhuriyar Nijar.