A cikin shirin za a ji cewar a birnin Maradi na Jamhuriyar Nijar an gudanar da wani taron mahawara kan tsattsauran ra’ayin adini da zamantakewa, yayin da a waje guda kuma ake shirin fara babban taron kolin kungiyar tarayyar Afirka AU a Yamai babban birnin kasar.