A cikin shirin za a ji cewa a Najeriya, kungiyoyi masu zaman kansu na kokarin ganin sun kawo karshen matsalar nan ta yawo mara amfani da 'yan mata ke yi mussaman a arewacin kasar. A Kwango kuwa, likitoci sun yanke shawarar tsaurara yajin aiki da suka shiga, lamarin da ke zama mai muni a fannin kiwon lafiya.