A cikin shirin bayan labaran duniya akwai rahoto kan zaben majalisa a Somaliya wanda mata ke son ganin an dama da su, sai rahoto game da wata matashiya a jihar Bauchin Najeriya da ta kirkiro sabon nau'i na maganin sauro da take sarrafawa daga kwalaye da wasu sinadarai. Akwai kuma rahoto game da shakkun da shugaban Tanzaniya ke nunawa a game da rigakafin corona.