A cikin shirin shirin za a ji cewa mabiya addinin kirista na bukukwan Ista ko Paques a bana a cikin gidajensu sabanin yadda aka saba yinsu a kowace shekara sakamakon yaduwar cutar nan ta Covid-19, a yayin da a Tarayyar najeriya wani matashi ya tallafa wa al'umma da abinci gami da kudade domin rage musu radadin yanayin da suka shiga na cutar Corona.