Shirin ya kunshi labaran duniya da kuma sharhunan bayan labarai wanda a cikinsa za a ji cewa wakilan manyan jam'iyyun siyasar Jamhuriyar ta Nijar a Kano da ke tarayyar Najeriya n sun fara gangamin tallata manufofin 'yan takararsu bayan da aka kaddamar yakin zabe a hukumance a ranar Asabar da ta gabata.