Baya ga labaran duniya, shirin ya kunshi rahotanni cikin shirinmu na sharhunan bayan labarai wanda a ciki za a ji cewa hukumomi a Nijar sun bankado wata badakala ta sayar da filotai ba bisa ka'ida ba. Shirin zai kai mu Najeriya da Ghana kana za a saurari rahoto na cikin salsalar rahotanninmu na Sauyi a Afirka.