Shirin na wannan safiya ta Lahadi ya mayar da hankali ne kan zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisa a Janhuriyar Nijar wanda ake farawa yau. Rahotanni da da Kalamazoo a jihar Michigan da ke Amirka na cewar wasu harbe-harbe da aka yi sun yi sanadin rasuwar mutane shidda da kuma jikkata wasu da dama.