A cikin shirin wanda ya kunshi labarai da rahotanni cikin shirin nan na sharhunan bayan labarai za a ji cewar akwai yiwuwar wasu daruruwan mahajjata daga jihar Filato a Najeriya su gaza samun damar zuwa yin aikin hajji bana. A Nijar kuwa hadin gwiwar kungiyoyin farar hula ne suka kafa wata kungiyar da za ta sa ido kan zaben shugaban kasa da za a yi a badi.