Bayan sauraren labaran duniya a cikin rahotanninmu za a ji cewa al'ummar jihar Zamfara na cigaba da nuna adawa da matakin hana 'yan majalisar jihar yin tsokaci kan matsalar tsaro a zauren majalisa, a yayin da a birnin Damagaram na Jamhuriyar Nijar mata sun bayyana gamsuwar su da yadda gayyar yaki da talauci ke ci gaba da yin tasiri biyo bayan tallafin kungiyoyin kasa da kasa.