Shirin ya kunshi ra'ayoyin 'yan Nijar kan taron da Faransa ta kira game da halin tsaro a yankin Sahel. A Najeriya akwai batun hadin kan bagarorin kasar shekaru 50 da kawo karshen yakin Biyafara. Akwai ma yadda almajirai ke fama da tsananin sanyi a arewacin Najeriyar.