A cikin shirin za a ji a Najeriya mutane masu bukata ta musamman sun koka ainun a kan kalubalen da suke fuskanta wajen rijistar katin dan kasa musamman a yanzu da aka tilasta samunsa ga duk wanda ke son ci gaba da amfani da wayar tafi da gidanka a kasar.