Cikin shirin za a ji cewa a yau ne shugaban Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar ke cika shekaru biyu a wa’adinsa na biyu. Sai bangarorin kasar na bayyana ra'ayoyi kan wa’adin na biyu kuma na karshe. Wasu sun ce sun gamsu, wasu kuwa cewa suke yi ba Nijar bata taba samun yanayi mafi tsananin wuya yanda ake ciki ba.