Cikin shirin na safe za a ji cewa kotun koli a Jamhuriyar Nijar,ta yi zaman yi wa Hama Amadou, tsohon kakakin majalisar dokokin kasar kuma madugun adawa, shara'a kan badakalar nan ta cinikin jarirai. A Najeriya kuwa an kai hare-hare ne kan sansanin 'yan gudun hijira da ke wajen birnin Maiduguri a yankin arewa maso gabashin kasar.