A cikin shirin za a ji cewa, shugabanni da gwamnatocin kasashen duniya na ci gaba da aika sakonnin ta'aziyyar bisa rasuwar Sarauniya Elizabeth ta II. Manoma a Najeriya na cike da fargaba da nuna damuwa dangane da yadda ambaliyar ruwa da kuma tsutsar nan mai canye amfanin gona ke kokarin kassara masu amfanin gonakkinsu.