A cikin shirin za a ji cewa 'yan boko da kuma masu fada aji na fulani sun dauki hanyar kawo karshen tashe-tashen hankula dama zubar da jinin da ke barazana ga makomar Najeriya. A Ghana ana matsa lamba ga mahukuntan kasar don su samar da kariya ga tsofaffin mata da ke fuskantar barazanar cin zarafi.