A cikin shirin za a ji cewa al'ummar jihar Taraba a Najeriya na zaman dar dar tun bayan da 'yan bindigar daji suka sanar da cewa za su farwa wasu garuruwan jihar, wanda hakan ke zuwa a daidai lokacin da rikicin shugabanci ya sake kunno kai a cikin jam'iyyar APC mai mulki a kasar.