A cikin shirin bayan labaran duniya za ku ji a Jamhuriyar Nijar ‘yan kasar na can yanzu haka na kada kuri’a a zaben kananan hukumomi da ke zama mataki na farkon na jerin zabukan gama gari da kasar ta shirya gudanarwa. A bangaren shirye-shirye muna dauke da Tushen Afirka da Ku Shiga Kulob da Darasin Rayuwa da kuma Afirka a Mako har ma da Wasikun Masu Sauraro.