A cikin shirin za a ji cewa rahotanni na nuni da cewa Sarkin Daura Umar Faruk Umar na kwance a babban asibitin gwamnatin tarayya dake birnin Katsina yana samun kulawar likitoci sakamakon zargin ya kamu da cutar coronavirus. a Nijar kuwa hukumomi sun bayyana kama wasu gaggan barayi da 'yan fashi da suka jima suna aikata ta'asa a wasu sassan kasar.