A cikin shirin za a ji cewa, a Najeriya majalisar wakilan kasar ce ta yi watsi da dokar nan da ke neman hallata kungiyar Peace Corps, a Nijar kuwa a wani matakin da ke zaman riga kafin rikice-rikice tsakanin makiyaya da manoma, hukumomi da kungiyoyi sun soma wani aiki na wayar da kannun al'umma domin kaucewa fadawa cikin riginginmun da ke janyo asarar rayukan jama'a.