A cikin shirin za ku ji cewa albarkacin ranar yaki da ci da gumin yara ta duniya ta 12 ga watan Yuni, kungiyoyin fafutikar kare hakkin yara kanana a Nijar sun yi korafi game da halin da yara kanana suke a kasar na sanya su aiki karfe da kuma yi masu fyade.