A cikin shirin za a ji cewa, a Nijar bangarorin siyasar kasar da suka hada da na kawancen masu mulki da na 'yan adawa ke mayar da martani game da sabon kawancen da tsohon Ministan harkokin wajen kasar ya kafa mai suna FPP, sabon kawancen ya bayyana shiga kafar wando guda da Gwamnatin shugaba Muhammadou Issoufou.