A cikin shirin za a ji cewa A Jamhuriyar Nijar akalla mutane da 40 ne suka gamu da ajalinsu sakamakon ambaliyar da aka fuskanta a 'yan kwanakin nan, a Najeriya kuwa shugabannin siyasa da sarakunan gargajiya da na Addinai sun gudanar da wani taron koli game da batu tabarbarewar tsaro a Kudu maso yammacin kasar.