Jamus ta soma daukar matakin karancin gas
March 30, 2022Jamus tayi kira ga kamfanoni da masana'antu dama sauran 'yan kasa da su yi kokarin rage yawan makamashin da suke amfani da shi, a kokarin da kasar ke yi don ganin ta daina dogaro da iskar gas da take siya daga Rasha. Sanarwar ta fito ne daga hannun Ministan tattalin arzikin kasar Robert Habeck da yayi gargadi kan irin kalubalen da kasar ke fuskanta bayan da Rasha ta nemi kasashen da ke siyan iskan gas daga gareta da su biya ta da kudin kasar na ruble.
Ba wai hakan na nufin an soma fuskantar karancin makamashin a Jamus in ji ministan amma yana daga cikin matakan farko da Jamus ta tanadar don shawo kan barazanar karancin makamashi a kasar. Batun cinikin makamashin da kudin Ruble na Rasha ya matukar harzuka Turai, amma Shugaba Vladimir Putin ya ce, bai ga wani abin tashin hankali a tsarinsa da ya ce, ba cuta ba cutarwa a sayar da makamashin da kudin kasar Rasha ba.