Shirin NATO na kara kashe kudin tsaro
June 25, 2025A birnin The Hague na kasar Netherlands da shugabannin kasashen kungiyar tsaron NATO/OTAN ke taro ake sa ran za su amince da gagarumin shirin kashe kudi a bangaren tsaro, wanda zai zama kari mafi girma tun bayan kawo karshen yakin cacar-baka, sakamakon rushewar tsohuwar Tarayyar Soviet. Karkashin sabon shirin kasashen kungiyar NATO za su kashe kimanin kaso 5 cikin 1000 na karfin tattalin arzikin kasashen a bangaren tsaro.
Karin Bayani: Shin Turai ta shirya kare kanta ba Amurka?
Shugaba Donald Trump na Amurka wanda zai gana da shugabannin kasashen a wajen taron, shi ne ya saka kaimi wajen ganin an kara kashe kudi a bangaren tsaron kasashen kungiyar NATO. Sannan yakin da gwamnatin Shugaba Vladimir Putin ta Rasha ta kaddamar kan kasar Ukraine ya kara zaburar da kasashen na kungiyar NATO, domin suna zargin Rasha tana takalar kasashen da neman fada.