Shirin dakatar da zirga-zirgar babura a Najeriya
July 22, 2022A lokuta da daman gaske a bangaren barayin dajin da ke cin karensu a dazukan da ke jihohin yankin na arewa na yin amfani da baburan wajen kai hare-hare. To sai dai kuma gwamnatin kasar ta ce tana shirin haramta amfani da baburan da nufin gurgunta hanyoyin sufuri na barayin dajin. Duk da kaurin sunan amfani da baburan wajen tada hankali, miliyoyi na 'yan kasar na dogaro bisa babura din domin harkar sufuri a kauyuka da sana'a ta acabar ke zaman hanyar rayuwar matasan kasar da daman gaske. Kuma ra'ayi na bambamta har a tsakanin masana bisa tasiri na shirin ga kokari na warware matsalar ta tsaro da ke shirin tarewa cikin kasar a halin yanzu. To sai dai in har hukumomi na jihohi sun yi nasarar haramta babura a birane can baya, daga dukkanin alamu da kamar wuya kai wa ga tsaida su a fadar Yusha'u Aliyu da ke zaman kwararre ga batu na tattali na arzikin da kuma ya ce baburan na zaman kashin bayan tattali na arziki a karkara. Ya zuwa karshen shekarar da ta shude dai Najeriyar na da babura sama da miliyan goma da ke da rijista kuma ke taka rawa iri-iri kama daga gurbata muhali ya zuwa ga taimaka wa tattali na arzikin al'umma ta kasar.