Shin Kwango za ta samu zaman lafiya?
June 30, 2025Shugaba Felix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ya bayyana cewa sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla domin kawo karshen rikicin gabashin kasar tare da kasar Ruwanda ta bude sabon sabin tarihi na samun kwanciyar hankali a yankin.
Karin Bayani:An cimma yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin Kwango da Ruwanda
Shugaban ya fadi haka a jawabin da ya gabatar ta kafofin yada labarai a wannan Litinin albarkacin cika shekaru 65 da samun 'yanci daga Turawan mulkin mallaka na kasar Beljiyam.
Yarjejeniyar da kasar Amurka ta taimaka aka kulla tana da nufin kawo karshen rikicin gabashin Jamhuriyar Diomukuradiyyar Kwango, inda mayakan 'yan tawaye na kungiyar M23 suka kwace wasu yankunan gabashin kasar, mayakan da ke samun goyon bayan kasar Ruwanda.