Shin 'yan Togo na iya zanga-zanga?
June 26, 2025Gwamnatin kasar ta Togo tuni ta fitar da sanarwar yin gargadi ga mutanen da suka shirya wannan zanga-zanga, wadanda zuwa yanzu suna nuna ko in-kula da gargadin na gwamnatin da ma matakin majalisar sarakunan gargajiya na cewa zanga-zangar 'yan fafutukar ta saba ka'ida. Inda wasu daga cikin masu rike da rarautar suka ce suna shirya da ganin sun hana wannan zanga-zangar adawa da gwamnati da ta saba ka'ida.
Karin Bayani: Cece-kuce kan mulkin 'yan gida daya a Togo
Togbui Lankivi, mai rike da sarautar Adakpamé mai tasiri a kasar ta Togo, da ke da aikin tabbatar da mutunta al'adu na cikin wadanda suka yi watsi da duk wani matakin zanga-zangar da ta gaba ka'ida. Kuma sun tabbatar da neman ganin ci gaba da zaman lafiya da mutuntua dokokin kasar.
Wannan kalamai sun haifar da muhawara a kasar ta Togo, inda wasu suke ganin haka a matsayin kiran neman tashin hankali. Matashi mai nazarin kan harkokin rayuwa kana mai kare hakkin dan Adam, Esso-Dong Kongah ke zama babban daraktan cibiyar kare hakkin dan Adam da bayar da hoto ta Togo, wanda yake ganin matsayin jagoran Adakpamé abin tsoro ne da ke tayar da hankali.
Duk da gargadin da gwamnatin kasar ta Togo ta yi kan fitowa zanga-zangar da ta saba ka'ida masu shiryawa suna ci gaba da gangami a shafukan intanet. Masana dokoki irin Esso-Dong Kongah na ganin ka'idojin kasashen duniya su ne a kan komai, na ganin gwamnati ta samar da damar yin zanga-zanga cikin tsanaki da kwanciyar hankali, ko sun sanar da hukumomi ko ba su sanar ba. Kuma haka ne ya dace da ka'idojin hukumar kare hakkin dan Adam ta kasashen Afirka.
Wannan yanayi ya zama matsala game da batun 'yancin yin zanga-zanga a kasar ta Togo da ke yankin yammacin Afirka.