Takarar Biya na fuskantar adawa a kudancin Kamaru
July 2, 2025Sun yi kira cikin wata budaddiyar wasika da aka yada a kafafen yada labarai da shafukan sada zumunta da ke cewa, kar a zabi Biya a zaben shugaban kasa na watan Oktoba mai zuwa sakamakon rashin kawo ci gaba a yankin kudancin tsawo shekarun da ya kwashe a kan madafun ikon kasar.
Mutum 8 ne suka rattaba hannu cikin wasikar ciki har da Farfesa Jean Calvin Aba Oyono malamin jami'a kuma masani a fannin shari'a. Yankin kudancin Kamaru wanda ke zama mahaifar shugaban kasa, ya kasance cikin mummunar hali sakamakon rashin ingantattun hanyoyi da rashin wutar lantarki da rashin ayyukan yi ga galibin matasa wadanda suka yi karatu, in ji Farfesa Jean Calvin Aba Oyono.
''Mun yanke shawarar gabatar da matsalolin 'yan yankin kudanci saboda mun lura cewa ana gabatar mana da kudancin kamar cibiyar siyasa wacce jam'iyya mai mulki ke cin karanta babu babbaka, inda babu adawa da mulkin Paul Biya, bayan kuwa siffofinmu na bayyana wahalhalu da muke fuskanta ku je mararrabar Ebolowa, Sagmelima bayan Mbalmayo hanyar da ke zuwa kauyen shugaban kasa ta lalace ina tambayar kaina ta yaya yake zuwa kauyensa da mota''.
Lucien Bedima dan jam'iyyar mai mulkin Kamaru ya ce Paul Biya ba shugaban kudanci ba ne kawai, shugaban Kamaru ne baki daya saboda fitowar wasu tsirarun 'yan kudanci na da alaka da kabilanci.
''Shugaban Kamaru Paul Biya ba shugaban kudancin Kamaru ba ne kawai, shugaban kasa ne ko da haifaffen kudanci ne kamar yadda Amadou Ahidjo yake haifaffen Garoua amma ya kasance shugaban Kamaru, kuma idan kudanci ya zabi ko ba ta zabi Paul Biya ba, zai lashe zabe saboda ba kudanci kadai ke zaban Paul Biya shugaban kasa saboda Paul Biya shugaban da duk al'ummar Kamaru ke mara masa baya''
Ga Farfesa Mathias Eric Owona Nguini masanin harkokin siyasa ya ce fitowar wasu daga cikin 'yan yankin kudanci abu ne da yake da alaka da siyasa, magoya bayan jam'iyyar adawa ta MRC ne.
''A yanzu muna cikin gwagwarmayar siyasa magoya baya da 'yan jam'iyyar MRC ne, wadanda suke gwagwarmayar siyasa duk da cewa ana samun wadannan matsalolin amma ba kamar yadda suke gabatarwa ba, domin idan ka saurare su kamar babu wani abin da aka yi a can wanda bai sani ba ne zai iya irin wannan magana, ada fita daga kauyena zuwa birni sai da muka kwashe sa'o'i hudu, amma yanzu muna kai kawo kamar yadda muke bukata ba, tare da wata matsala ba''.
Baraka da a kan samu tsakanin yan yankin kudancin Kamaru na zuwa ne daidai lokacin 'yan arawancin Kamaru ke juya wa Paul Biya inda aka samu jiga-jigan siyasa biyu Bello Bouba Maigari da Issa Tchiroma Bakary suka raba gari da Paul Biya suka sanar da tsayawa takarar zaben shugaban kasa.