Shugaban Chadi na ziyara a Jamhuriyar Nijar
August 6, 2025Wannan ziyara ta kwanaki biyu da za ta kai shugaban Chadi Mahamat Idriss Deby zuwa makwabciyar kasar Jamhuriyar Nijar na daukar hankalin masu sharhi kan al'amuran yau da kullum domin tana zuwa ne a daidai gabar da wasu kasashen yankin Sahel ke neman cikakken 'yanci bayan raba gari da Faransa da ta yi musu mulkin mallaka.
Duk da cewa dai ba a fayyace ajandar wannan ziyara a hukumance ba, wasu masharhanta na tunanin cewa Shugaba Deby da takwaransa Janar Abdourahamane Tiani za su mayar da hankali kacokan kan muhimman batutuwa da ke ci wa kasashen biyu da ma yankin Sahel tuwo a kwarya.
Karin Bayani:Kulla alakar tsaro tsakanin Chadi da Nijar
A mahangar Remadji Hoinathy mai bincike kan al'amuran siyasa a Chadi, da akwai yiwuwar shugabannin biyu sun tattauna kan karfafa alaka a tsakanin N'Djamena da kasashen kungiyar AES wadda ta kunshin Jamhuriyar Nijar da Mali da Burkina Faso wadanda suka juya wa kungiyar ECOWAS baya bayan raba gari da tsohuwar uwar gijiyarsu Faransa. To sai dai a mahanagar mai sharhi kan harkokin siyasa a Chadi Narcisse Laldjim, batutuwan tsaro da na tattalin arziki za su kasance manyan maudu'ai da shugabanin biyu za su mayar da hankali a kai.
Dadin dadawa ma masharhancin ya kara da cewa akwai yiwuwar shugaba Deby da takwaransa Janar Tiani su canja yau kan shirin gina bututun fitar da danye mai wanda zai hada Nijar da Chadi da kuma Kamaru mai da ke da gabar Teku.
Wannan ziyara dai ta shugaba Mahamat Idriss Deby na zuwa ne shakeru biyu bayan tafiyarsa birnin Yamai washegarin juyin mulkin da ya hambarar da gwamnatin farar hula ta Mohamed Bazoum en watan Yuli na 2023.
A wancan lokaci dai taron shugabanni kasashen kungiyar ECOWAS ne ya aike da shugaba Deby zuwa Nijar din domin tattaunawa da sojojin da suka kifar da gwamnati domin sakin hambararren shugaba kasar Mohamed Bazoum, sai dai ba tare da haka cimma ruwa ba.