Matakin neman bunkasa abinci a Najeriya
January 14, 2025A cikin yanyi na wuya miliyoyin al'ummar Najeriya suka kai zuwa kaka ta bana, sakamakon hauhawa dama karanci na abinci a birane da kauyukan tarayyar Najeriya. Kasar da ta kalli hauhawar d akai kusan kaso 40 cikin dari a da#amin, a karon farko cikin shekaru 40 da doriya. To sai dai kuma masu mulkin Najeriya sun ce sun nisa wajen batun matakai da nufin kaucewa matsalar da ke zaman barazana mafi girma.
Karin Bayani: Fargabar samun karancin abinci a Najeriya
Ministan noma na kasar senata Abubakar kyari dai yace kama daga taraktocin noma zuwa ga batun iri da taki na zamani, Abujar da hadin gwiuwar jihohi na kasar daban daban sun nisa a kokarin kawo sauyi a cikin harkar noma na kasar.
To sai dai koma ya zuwa ina ake shirin zuwa a kokarin kaucewa jiya dai, kasar ta yi amai ta kuma lashe a shekarar da ta shude yayin da ta ce tana shirin sayo abincin waje, amma kuma ta gaza kai wa zuwa cikon alkawarin. Kuma ministan ya ce haka na da ruwa da tsaki a kokarin kare manoma na kasar.
Koma ya zuwa ina Abuja ke neman kai wa da nufin burge masu sana'ar noman dai sababbin matakan daga duk alamun tana shirin karin damara kan tunkarar rashin tsaro a tunanin Kabir Ibrahim da ke zaman shugaban haddaddiyarkungiyar manoman Najeriya AFAN, wanda ya ce samar da tsaro zai yi tasirin wajen tabbatar da abinci ya wadaci kasar.
Abun jira a gani dai na zaman matakin gaba ga masu mulkin kasar da suke shirin fuskantar jarabawar talakawan da ke fadin suna da bukata ta abinci. Tarayyar Najeriya dai ta ce tana shirin girbe alkama.