Matsayin Saudiyya kan samar da 'yancin Falasdinu
August 6, 2025
Wasu na ganin wannan mataki wata dabara ce ta diflomasiyya da ka iya kawo zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya. Amma wasu na ganin wata hanyar farfado da martabarta ne a idon duniya bayan matsin lambr da kasar ke fuskanta kan batun 'yancin dan Adam.
Wannan ba shi ne yunkuri na farko da Saudiyya ta yi domin samar da kasar Falasdinu ba. A makonnin baya, Saudiyya da Faransa sun jagoranci wani taro a birnin New York kan batun kafa Falasdinawa a matsayin kasa.
Bayan taron, kasashe irinsu Faransa, Kanada, Malta, Birtaniya da Ostareliya sun bayyana cewa za su amince da Falasdinu ko kuma suna duba yiwuwar hakan.
Karin Bayani: Taron Larabawa kan makomar Gaza a Masar
Taron ya fitar da wata matsaya mai suna "New York Declaration", inda kasashe 22 na kungiyar Larabawa suka rattaba hannu, tare da Tarayyar Turai da wasu kasashe fiye da 17 domin yi wa tufkar hanci- kasar Isra'ila dabanm, kasar Falasdinawa dabam.
Haka kuma, taron ya bukaci kungiyar Hamas ta ajiye makamai, ta saki fursunoni kuma ta sauka daga sha'anin gudanar da mulki a Zirin Gaza.
Kazalika matsayar da kasashen suka cimma ta nuna damuwa kan yadda Isra'ila ke kai hari kan fararen hula da hana kayan jin kai shiga Gaza, wanda hakan ke kara tsananta halin da al'umma ke ciki.
Masana sun ce wannan wani mataki ne wanda ba a saba gani ba, inda kasashen Larabawa suka fito fili suka soki Hamas. A bisa wannan dalili ne Saudiyya da Faransa ke shan yabo da jinjina kan cimma wannan matsaya.
To shin me ya sa Saudiyya ta bijiro da wannan sabon salo?
Wannan yunkuri ya fara tun watan Satumba na 2024, lokacin da Saudiyya da Norway suka kafa wata gamayya ta kasa da kasa domin aiwatar da tsarin kafa kasa biyu. Kasashen Turai da Majalisar Dinkin Duniya sun mara wa shirin baya.
Amma dalilin Saudiyya ba wai jin kai kawai ba ne. Masana sun ce akwai manufa ta siyasa a ciki.
Kafin harin Hamas na Oktoba 2023, Saudiyya na kokarin gyara huldar diflomasiyya da Isra'ila. Wannan ya janyo cece-kuce daga kasashen Larabawa da ke ganin Saudiyya ta na nuna alamun watsi da Falasdinu. Yanzu, wasu na ganin wannan sabon yunkuri wani kokari ne na Saudiyya don dawo da martabarta.
To amma wasu masana irinsu Aziz Alghashian na gamayyar Gulf International Forum da ke duba al'amauran kasashen Larabawa sun ce sha'awar Saudiyya na hulda da Isra'ila ba sabon abu ba ne — tun shekarun 1960 take wannan yunkurin.
Haka kuma, Saudiyya na goyon bayan kafa Falasdinu tun shekaru da dama. A 2002, Saudiya ta gabatar da "Tsarin Zaman Lafiya na Larabawa", wanda ya bukaci Isra'ila ta janye daga yankunan da ta mamaye domin a kafa Falasdinu.
Yanzu dai, matsayar da aka cimma New York ana ganin ta tamkar wancan tsarin na 2002, aka kakkabe, aka dawo da shi ya zama sabo.
Masana sun ce Saudiyya na da muradun cikin gida da na ketare da ke sa ta daukar wannan mataki.Daya daga ciki shi ne bukatar zaman lafiya a yankin domin ta samu aiwatar da shirin bunkasa tattalin arziki musamman wajen rabuwa da dogaro da man fetur.
Baya ga haka, Saudiyya na neman karin tasiri a siyasar duniya. Wasu kafafen yada labarai sun ce Saudiyya na amfani da wannan yunkuri don kafa karfin siyasa a tsakanin kasashen Larabawa da Musulmai da kuma samun tasiri a batun makamashi da harkokin tsaro.
Wannan yunkuri zai kai ga gaci?
Har yanzu ba a san ko wannan yunkuri zai yi tasiri ba. Amma alamun sauyi sun fara bayyana.
Ministan Harkokin Wajen Saudiyya, Faisal bin Farhan, ya bukaci karin kasashe su mara wa wannan shiri baya kafin babban taron Majalisar Dinkin Duniya a watan Satumba.
Masana sun ce shirin zai iya amfani wa Amurka, Isra'ila da yankin gaba daya idan har ana son warware rikicin da ya dade yana janyo asara da tashin hankali.
Amma Isra'ila da Amurka sun ki halartar taron New York, kuma sun soki matakin. Jakadan Isra'ila ya ce ana gudanar da wani taro ne da bai da nasaba da gaskiyar abin da ke faruwa a kasa.
Ko wannan yunkuri na Saudiyya yana da niyyar kawo zaman lafiya ne, ko kuma wata dabara ce ta siyasa, abu daya ya tabbata? Masu sharhi na cewa Saudiyya na kokarin janyo hankalin duniya ta hanyar shiga tsakani kan batun Falasdinu kuma kowa na kallon ta.