Hanyoyin magance matsalolin tsaron Najeriya
August 22, 2025Babban hafsan tsaron Janar Christopher Musa dai ya ce siyasar shekarar 2027 da a karkashinta ake neman dusashe ci gaban gwamnatin kasar dai ce ke jawo sake ta'azzarar rashin tsaron a halin yanzu. Daruruwan 'yan kasar ne dai ake kisa a duk wata sakamakon rashin tsaron da ke nuna alamun wucewa da sanin jami'an tsaron kasar.
Karin Bayani: Najeriya: 'Yan Boko Haram 129,417 sun mika wuya
Kama daga Katsina ya zuwa ga Zamfara da Sokoto, ko bayan Benue da Plateau dai sannu a hankali Najeriya tana kallon karuwar kisa na rayuka cikin kasar a halin yanzu. To sai dai kuma karuwar harin da ke zuwa a lokacin da fagen siyasar Najeriya yana dada zafi dai tuni ya fara kaukar launi irin na siyasa a kasar
An dai ruwaito babban hafsan tsaron kasar Janar Christopher Musa ya na ta'allaka harin da bakar siyasa ta kasar da ke kadawa yanzu. Janar Musa dai ya ce masu kokarin dakushe nasara ta gwamnatin kasar a zabe na gaba ne ke da hannu a karuwar ta'azzarar rashin tsaro a halin yanzu. Zargin kuma da a cewar Sanata Umar Tsauri da ke zaman jigo a cikin jam'iyyar PDP ta adawa ke kama da zalunci na kokarin dorawa kare laifin kura.
Kokarin siyasa da tsaro, ko kuma neman kafa tarihi dai, batun rashin tsaro da kila tattalin arziki dai, daga duk alamun zaman batutuwa na kan gaba cikin siyasar ta gaba. Kuma kalaman Janar Musan cikin tsaron na da bukata ta bayanai ga 'yan kasar da ke neman amsar matsalar rashin tsaron a tunanin Dr Faruk BB Faruk da ke sharhi cikin batun na siyasa.