Najeriya: Shekaru 58 da samun 'yanci
October 1, 2018
Wannan ne karon farko a cikin shekaru takwas da Najeriyar ke buga kirji na bikin ranar 'yancin a Dandalin Eagles Square da ke zaman babban zauren taro na kasar. Duk da wani hatsarin jirgin saman sojan kasar a yayin atisaye, an yi nasarar gudanar da faretin da ya samu halartar daukacin jami'an tsaro da kuma manyan baki daga ciki da ma wajen kasar.
Tun bayan wani harin bam na ranar 'yancin a shekara ta 2010 ne mahukuntan Najeriyar suka koma kuryar daki, inda suke bikin a cikin fadar gwamnatin kasar a duk shekara. Shugaba Buhari a wajen wani jawabin da kila ke zaman na karshe kafin a gudanar da zabukan kasar a shekarar da ke tafe, ya ce an cimma nasarori da dama kama daga yaki da cin hanci ya zuwa na ta'addanci a shekaru uku da doriya na mulkinsa.
Ya kara da cewa, sun gina hanyoyi da layin dogo na zamani da makarantu, sun kuma bunkasa fannin makamashi da tashoshin jiragen sama dana ruwa. Najeriya na shirin sake gwajin farin jini da ci gaban mulkin a wajen zaben kasar da ke tafe a cikin watan Fabrairu na na shekara mai zuwa ta 2019.