Shekaru 50 na diplomasiyyar EU da China
July 24, 2025Kasashen Turai da China sun shafe shekaru suna gudanar da harkokin kasuwanci cikin lumana kafin dambarwar haraji da ta kunno kai daga Amurka.
Tuni dai wakilan EU da suka hadar daShugaban Majalisar Tarayyar Turai António Costa da Shugabar Hukumar Zartarwa ta Kungiyar Ursula von der Leyen suka fara taba alli da hukumomin China a birnin Beijing. Alaka ce dai mai cike da tarihi duk da cewa EU na da ‘yan korafe korafe kan bukatar sassauta wasu shingaye na kasuwanci, wanda ko a bara an yi cinikayya ta sama da Euro biliyan 305.8 kwatankwacin dala ($360) tsakanin China da Tarayyar Turai.
Karin bayani: EU da China na taron cika shekaru 50 da kulla diflomasiyya
Von der Leyen da shugaban majalisar kungiyar ta EU Antonio Costa sun gana da shugaban kasar China Xi Jingping domin cimma matsaya kan ajandar taron mai matukar muhimmanci da suka hada da diflomasiyyar kasuwanci da kuma matsayar China kan yakin Rasha da Ukraine har ma da halin da kasashen ke ciki game da barazanar haraji daga Amurka.
Shugaban China ke nan Xi Jinping Inda yake cewa "Da zarar kasashen duniya sun dunkule a matsayin tsintsiya wajen cimma muradunsu to babu shakka za su samu saukin gudanar da al'amura ba tare da tashin-tashina ba, kuma da zarar China da EU suka karfafa mu'amala da fahimtar juna da kuma hadin kai to tabbas duniya za ta shaida kyakkyawar alakar da ke tsakanin China da Tarayyar Turai''.
Karin bayani: Kungiyar EU za ta kara haraji ga manyan kamfanonin fasahar Amurka
A nata jawabin Shugabar Hukumar Zartarwa ta Kungiyar Ursula von der Leyen ta yi waiwaye kan alakar da ke tsakani da kuma bukatar daga kambun diflomasiyyar kasashen domin kasancewa gagara-gasa.
"A yau, Turai da China ne ke rike da 2/3 na karfin tattalin arzikin duniya da kuma hada-hadar kasuwanci, kuma dangantakarmu na daya daga cikin alaka mafi girma tsakanin kawaye a fadin duniya''.
A na shi bangaren shugaban hukumar Tarayyar Turai António Costa ya bukaci China da ta yi amfani da buwayarta wajen kawo karshen yakin Ukriane.
"A matsayin China na mai rike da kujerar dindindin a Majalisar Dinkin Duniya, muna kira ga Beijing da ta yi amfani da damarta wajen shawo kan Rasha kan martaba dokokin Majalisar kuma ta kawo karshen mamayar da Rasha ta yi a Ukraine''.
Yanzu dai kallo ya koma birnin Beijing na kasar China kan batun yaukaka dangantakar kimanin shekaru 50, wanda ke fuskantar tazgaro kan bambancin ra'ayin kasuwanci da kuma haraji har ma da matsin lamba ta kowanne bangare.