Shekara bayan zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriya
August 1, 2025Kungiyar kare hakin jama'a ta Amnesty International ta bayyana damuwa ne a kan abinda ta kira gaza yiwa mutane 24 da aka ‘yan sanda suka kashe adalci bayan gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa a Najeriyaar. Kungiyar ta sake dago wannan batu ne bayan cikar shekara guda da gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwar da aka gudanar a ranar 1 zuwa 10 ga watan Augustan 2024 inda ta bayyana cewa shaidu na gani da ido sun tabbatar da cewar ‘yan sanda sun kashe mutane 24 a jihohin Kano, Jigawa, Katsina da Borno. Mallam Isa Sanusi shine shugaban kungiyar kare hakin jama'a da Amnesty International a Najeriya.
Karin Bayani: Zargi 'yan sanda da cin-zarafi a Najeriya
'Yan uwan mutanen da suka shiga zanga-zangar sun kasance cikin hali na juyayi inda har zuwa wannan lokaci babu diyyar da aka biya da zata iya rage masu radadi na rashin 'yan uwan da suika yi a lokacin zanga-zangar. Comrade Yahya Abdullahi na cikin wadanda suka sha da kyar a lokacin da aka yi zanga-zangar.
Tuni gwamnatin Najeriyar ta yankewa mutane biyar da suka shiga zanga-=zangar hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari a Maidugurin jihar Borno. Amnesty International ta ce duk da shaidu da suka nuna a fili babu laifin da suka aikata. Kungiyar ta Amnesty Intwernational ta dage kan cewa ‘yan sanda sun kashe mutane a lokacin zanga-zangar don sun yi amfani da karfin da ya wuce kima. To sai dai ‘yan sanda na Najeriya sun nan kan bakarsu ta musanta wannan zargi.
Kungiyar ta Amnesty International na mai kashedin hatsarin da wannan ke da shi ga rayuwa da zamantakewar alumma. Hari la yau ga Mallam Isa Sansi shugaban kungiyar kare hakin jama'a ta Amnesty International a Najeriya.
Duk da hallaci da kundin tsarin mulkin Najeriyar ya bayar na ikon gudanar da zanga-zangar lumana ga ‘yan kasar don bayyana ra'ayoyinsu a kan abubuwan da gwamnati ke yi. A yanzu dai an kai hali da kiki kaka a tsakanin kungiyar Amnsety International da gwamnatin Najeriyar a kan wannan lamari.