Sharhin Jaridun Jamus a kan nahiyar Afirka
April 4, 2025
Jaridar die Tageszeitung ta ce kasashen Yuganda da Ruwanda duk suna cikin yankin gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango mai fama da tashe-tashen hankula. Kuma Ruwanda kai tsaye take goyon bayan 'yan tawayen kungiyar M23, yayin da sojojin Yuganda suke fada da wasu kugiyoyin tsageru, inda ake iya ganin daga bangaren kogin Kisangani.
A nata bangaren die Welt ta yi sharhin cewa Shugaba Yoweri Museveni na Yuganda wanda ya yi suna wajen kwadaita wa 'yan kasar samun ci-gaban tattalin arziki. Akwai lokacin da shugaban ya shaida wa dalibai aikinsu ne su haihu, kuma amfani da tsarin haihuwa wani mataki ne na kassara yawan al'umma. Yuganda tana samun karuwar al'umma na kaso 3.1 cikin 100 inda take daya daga cikin kasashen duniya da ke kan gaba wajen samun bunkasar al'umma. Sai dai a kasashen Afirka akwai kasashe irin Tanzaniya da Najeriya da 'yan siyasa ke wayar da kan al'umma bisa fa'idar tsarin iyali na tazara a wajen haihuwa. Yayin da a Ruwanda gwamnati ta yi fito na fito da Cocin Kiristoci mabiya Katolika kan yadda suke zagon kasa ga shirin gwamnati na samar da tsarin iyali.
A daya bangaren jaridar Neue Zürcher Zeitung ta duba yadda kasar Senegal take kara daukar matakan janyewa daga kasashen Yammacin Duniya, amma tana tare da masu juyin mulki, inda shugaban kasar yake nisanta kansa daga Faransa wadda ta yi wa kasarsa mulkin mallaka. Shugaba Bassirou Diomaye Faye na kasar ta Senegal wanda ya shafe shekara guda kan madafun ikon kasar da ke yankin yammacin Afirka. Shugaban mai shekaru 44 da haihuwa ya lashe zaben shekarar da ta gabata jim kadan bayan an sako shi daga gidan fursuna. Duk da yake ba sananne ba ne kan harkokin siyasar Senegal amma ya kayar da Firaminista Amadou Ba, wanda yake da goyon bayan tsohon Shugaba Macky Sall. Kuma kasar ta kasance tilo a yankin yammacin Afirka da sojoji ba su taba kwace mulki ba.
Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung ta mayar da hankali kan yadda Isaias Afewerki yake ci gaba da mulkin kama karya a kasar Eritrea da ke gabashin Afirka salon irin mulkin da ake gani a kasar Koriya ta Arewa. Mai shekaru 79 da haihuwa ya shafe fiye da shekaru 30 kan madafun ikon kasar ta Eritrea. Ofishin mai gabatar da kara na gwamnatin Eritrea na zargin wasu 'yan kasar da neman hargitsa lamura.
Ita kuma Welt online ta mayar da hankali ne kan yadda aka gano wata yarinya 'yar Somaliya 'yar shekaru 8 da haihuwa ba zato ba tsammani, bayan ta bace sakamakon auren dole da aka yi mata watannin da suka gabata. 'Yan gwagwarmaya suka gano yarinyar sakamakon gangamin da suka kaddamar a kafofin sada zumunta na zamani. Watanni shida da suka shude Fatima ta bace bayan auren dole, kuma yanzu haka ana bincike bayan gano ta a yankin Puntland na Somaliya wanda ya balle inda wani ya aure ta.