Sharhin Jaridun Jamus a kan nahiyar Afirka
February 14, 2025Jaridar die tageszeitung ta yi zumudi a sharhinta, tana mai cewa "Yakin Sudan ya kusa zuwa karshe." Wannan kuwa ba ya rasa nasaba da nasarar da sojojin gwamnati suka samu a kan mayakan sa kai na RSF a Khartoum babban birnin kasar. Jaridar ta ruwaito cewar kusan shekaru biyu da fara yakin da ya haifar da matsalar 'yan gudun hijira mafi girma da kuma matsalar yunwa mafi muni a duniya, dakarun gwamnatin Sudan sun kama hanyar ganin bayan mayakan da ke biyayya ga tsohon mataimakin shugaban gwamnatin mulkin soja Mohamed Hamdan Daglo da aka fi sani da suna Hametti.
die tageszeitung ta kara da cewa idan hakar dakarun Janar Abdelfattah al-Burhan AIdan ta cimma ruwa na fatattakar 'yan RSF daga khartoum, babu makawa gwamnatin Sudan za ta iya ayyana samun nasara a wannan yaki. Sai dai, bangarorin biyu na ci gaba da bata kashi a titunan birnin Khartoum inda suke amfani da manyan makaman atilari ba tare da la'akari da kare rayukan fararen hula ba. Jaridar wadda ake wallafawa a kullum a Jamus ta ce kashi biyu bisa uku na mazauna birnin sun kaurace wa matsugunansu. A yanzu haka ma dai, kashi biyu bisa uku na yawan jama'a a Sudan na dogara da taimakon gaggawa na jin kai don kauce wa ja'ibar 'yunwa.
Su kuwa sauran jaridun sun ci-gaba da bibiyar halin da ake ciki a gabashin kwango, inda 'yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Ruwanda ke cin karensu ba tare da babbaka ba. Jaridar ZEIT ONLINE ga misali ta yi sharhi mai taken " 'Yan bindiga sun kori dubban 'yan gudun hijira daga Goma na gabashin Kwango." Jaridar ta ce an shiga halin zullumi a gabashin Jamhuriyar Dimikuradayyar Kwango mai arzikin albarkatun kasa, bayan da 'yan tawayen M23 suka yi barazanar sake kai hari tare da mamaye birnin Bukavu. ZEIT ONLINE ta kara da cewar mayakan M23 na dirar mikiya a kan sansanonin gudun hijira tare da dibar musu wa'adin sa'o'i 72 domin su san inda dare ya yi musu.
A yayin da take nata tsokaci, jaridar Welt online ta mayar da hankali kan mummunan hali da mata da kanana yara ke ciki a yankin gabashin kwango da ke fama da rikici. Ta ce an sace mata yayin da aka yi wa wasun su fyade, a daya hannun kuma ake bautar da wasun su a Gabashin Kwango inda cin zarafi ke ci gaba da bayyana. Welt Online ta ce 'yan tawaye sun mamaye birnin Goma mai yawan jama'a miliyan daya, kuma akwai rahotannin da ke nuna cewar kisan gilla da musguna wa fararen hula na neman zama ruwan dare. An ce hatta sojojin gwamnati na da hannu a keta hakkin bil adama.
A nata bangaren, Neue Zürcher Zeitung ta mayar da hankali ne kan irin gwagwarmayar da tsohon shugaban Namibiya Sam Nujoma ya yi wajen 'yantar da kasarsa daga mulkin mallaka na Jamus. A sharhin da ta yi mai taken "daga kiwo zuwa uban kasa a Namibiya" bayan mutuwar tsohon shugaban Namibiya yana da shekaru 95 a duniya, jaridar ta danganta Sam Nujoma da dan fafutukar da ya shafe shekaru masu yawa yana gudun hijira domin samar wa kasarsa 'yancin kai. Hasali ma, hakarsa ta cimma ruwa inda bayan da ya koma gida a 1989, ya kasance shugaban kasa na farko na sabuwar kasar mai cin gashin kanta.
Neue Zürcher Zeitung ta ce marigayi Sam Nujoma ya fito ne daga gidan manoma a arewacin Namibiya, inda tun yana yaro ya rungumi kiwon shanu da awaki, lamarin da ya haifar masa da tasgaro a fannin ilimi. Sai dai bayan da ya fara aiki a kamfanin jiragen kasa, Nujoma ya fara adawa da matakan danniya na farar fata na Jamus, lamarin da ya sa ya shiga siyasa. Jaidar ta kara da cewa bayan da ya yi ta matsa wa Majalisar Dinkin Duniya lamba da ya kai ta ga sanya Namibiya a karkashin kulawarta, Afirka ta Kudu ta yi watsi da wannan mataki. Wannan ne ya sa kungiyarsa ta SWAPO ta fara gwagwarmaya da makamai domin cire wa kasarsa kitse a wuta.
Za mu karkare da sharhin Neue Zürcher Zeitung wacce ta ce matakin Shugaba Trump na Amurka na daina ba da agajin kasashen waje, kira ne na ankararwa ga Afirka. Jaridar ta ce a fili yake cewar za a samu karancin kayan masarufi a Sudan da yaki ya daidaita sakamkon katse tallafin Amurka, yayin da Yuganda da Afirka ta Kudu za su daina raba magungunan yaki da kwayar cutar Aids/Sida. Su kuwa ma'aikatan lafiya 40,000 a Kenya mai yiwuwa su rasa ayyukansu, saboda Donald Trump ya ba da umarnin dakatar da aikin taimakon kasashen waje. Jaridar ta ce idan Bera na da sata, Daddawa ma na da wari, inda ta ce gwamnatocin Afirka ma na da nasu laifin, saboda suna dogara ne a kan kudin agaji wajen aiwatar da tsarin kiwon lafiya da ilimi. Neue Zürcher Zeitung ta ce lokaci ya yi da gwamnatoci Afirka za su tsaya a kan kafafunsu wajen ciyar da al'ummarsu gaba.