Senegal ta yi dokar kare masu fallasa badakala a yanar gizo
August 26, 2025Gwamnatin Senegal ta amince da wata doka da za ta ba da kariya ga masu gwagwarmaya a shafukan sada zumunta, a kokarin tabbatar da gaskiya da shugabanci na gari, kamar yadda ta alkawarta yi kafin zuwanta kan madafun iko.
Dokar wadda majalisar dokokin kasar ta kada kuri'ar amincewa da ita a wannan Talata, ta tandi bayar da cikakkar kariya ga masu bankado laifukan cin hanci a hukumomin gwamnati da masu zaman kansu da kuma duk wasu kura-kurai da ake tafkawa wajen tafiyar da jagorancin al'umma.
Hakazalika dokar ta tanadi bai wa masu fafutika a shafukan sada zumunta tukwici na kashi 10% na adadin kudi da kuma kadarori a duk lokacin da suka bankado wata badakala.
Senegal dai ta zama kasa ta farko da ke samar da irin wannan doka a kasashen Afirka da ke kudu da hamadar Sahara, kuma tuni 'yan gwagwarmaya suka bayyana dokar a matsayin gagarumin ci gaba ga dimokuradiyya.